Game da Derek Prince | Derek Prince Ministries Nigeria (2024)

Table of Contents
Derek Prince Abubuwan da ke ciki

Derek Prince

Ma'aikata:

Shararren Malamin Littafi Mai Tsarki da ya taba duniya, marubuci, Mai wa'azi da masanin tauhidi

Haihuwa:

Mutuwa:

24 Satumba 2003 (shekaru 88), Jerusalem, Isra'ila

Abubuwan da ke ciki

(Danna don gungurawa zuwa wuri)

  • Haihuwarshi da farkon tashin sa
  • Yaƙin Duniya na Biyu
  • Lydia Prince
  • Ruth Prince
  • Mutuwa
  • Malamin Littafi Mai Tsarki
  • Derek Prince Ministries
  • Kalmonin Hikima na Derek Prince
  • Jerin Littattafai

Haihuwarshi da farkon tashin sa

An haifi Derek Prince a shekara ta 1915 a wani gari maisuna Bangalore a kasar Indiya, a lokacin da Mahaifinsa ke aiki da sojojin Burtaniya . Yana da shekara 14 da ya sami gurbin karatu a Kwalejin Eton inda ya karanta Greek da Latin. Ya ci gaba da karatunsa a Jami’ar Cambridge ta kasar Ingila, inda ya samu gurbin karatu a fannin Ilmin Falsafa na zamanin da, da na yanzu a King's College. Derek ya kuma karanci yarukan zamani da dama yayin da yake Jami'ar Cambridge, wadanda suka hada da Ibraniyanci da Aramaic, wadanda daga baya ya tace su a Jami'ar Ibraniyanci da ke Birnin Kudus.

Ko da yake Derek ya girma a cikin Ekklesia ta Anglican, ya watsar da horon da aka yi masa a yayin da ya ke a Jami'ar Cambridge, ya ɗauki ra'ayin duniya na rashin yarda da Allah. Da yake waiwaye a kan wadannan shekarun baya na karatu a manyan jami'u, daga baya ya ce:

“Na san kalmomi masu tsawo da jimloli da dama, kuma na gwada abubuwa da yawa. Amma, in na waiwaya baya, zan ga cewa na rikice, rai na ya baci, cike da takaici, kuma ban san inda zan sami amsa ba.”

Yaƙin Duniya na Biyu

An katse aikin karatun Derek a farkon barkewar yakin duniya na biyu. A shekara ta 1940 ya shiga soja a matsayin soja marar shiga daga, Don ya ci gaba da nazarinsa sa’ad da yake hidimar soja, Derek ya tafi da Littafi Mai Tsarki. wanda a lokacin ya dauke shi a matsayin aikin falsafa ne a maimakon hurarren nassi daga wurin Allah.

A ranar 31 ga Yuli 1941, lokacin da ya ke a barikin horon aikin soja a Scarborough, Yorkshire, ya sami babbar saduwa da Yesu wanda zai canza yanayin rayuwarsa. Da yake tunawa da abin da ya faru ya ce:

“Na ji muryar Yesu, yana magana sarai ta wurin nassoshin Littafi Mai Tsarki. Kuma tun daga ranar da na ji muryarsa, har zuwa yau, akwai abubuwa biyu da ban taba shakkar su ba. Ban taɓa shakkar cewa Yesu yana da rai ba, kuma ban taɓa shakkar cewa Littafi Mai Tsarki Kalmar Allah ne ba.”

Farkon tafiya ta ruhaniya kenan ta ɗaya daga cikin shahararrun malaman Littafi Mai Tsarki na wannan zamani

Kusan nan da nan bayan tuban sa, Derek ya koma da aiki a cikin hamada ta Arewacin Afirka inda ya kwashe shekaru uku yana aiki a assibitin soja. Ya keɓe lokacin hutawar sa don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da yin girma a cikin ruhaniya

A ƙarshen yaƙin, Derek ya yi murabus daga aikin soja yayin da yake a Urushalima, yana mai shaidar cikar annabcin Littafi Mai Tsarki na komawar Yahudawa zuwa kasar su ta Isra’ila.

Lydia Prince

A shekara ta 1946, Derek ya auri matarsa ​​ta farko, Lydia Christensen, ’yar ƙasar Denmark da ke kula da wasu marayu kusa da Urushalima. Ta haka ya zama uba ga ‘yan mata takwas da ta dauko riko

Derek da Lydia sun zauna a birnin Urshalima har zuwa bayan kafawar daular Yahudawa ta Isra'ila a shekara ta 1948. Yaki ya barke tsakanin sojojin Larabawa da na Isra'ila a lokacin yakin 'yancin kai. Suka bar kasar ba tare da son rai ba zuwa Ingila. Da zarar samun mazauni a tsakiyar London, Derek ya fara wa'azi a wani wuri da ake kira Speaker's Corner a Hyde Park, yawanci tare da matarsa Lydia da wasu daga cikin yaran su 'yan mata. Bayan wani lokaci sai suka fara gayyato masu saurare zuwa gidan su don karin koyaswa, ta haka su ka kafa sabuwar ekklesia. Wannan ya ci gaba har zuwa 1956 lokacin da Prince ya amsa kiran Allah, ya koma Kenya don aikin mishan a cikin watan Janairu shakara ta 1957.

A cikin shekarun da suka biyo baya, Derek da Lydia sun samu nasara da yawa sa’ad da suke yi wa mutanen yankin hidima, har ma da wata yarinyar da aka tayar daga matattu ta wurin addu’a.

A shekara ta 1962, Derek da Lydia sun ɗauko rikon wata marainiyar janjira daga kasar Kenya, a lokacin da suka je hutu a Canada. Lydia, wadda ta girmi Derek da shekara 25, ta cika shekaru saba’in kenan, ta yi marmarin ta zauna kusa da abokai da sauran masu bi. Da wannan bukata ta motsa shi, Derek ya karɓi gayyata ya zama malamin koyarda Littafi Mai Tsarki a wata ekklesia da ke Minneapolis.

Derek da Lydia Prince.

Amma kafin ƙarshen shekaru goma, Iyalin Prince sun chanza wurare sau uku; Seattle, Chicago da Fort Lauderdale, bi da bi. Cin gaba da suka samu a hidima ya buɗe sababbin ƙofofi da ba a yi tsammani ba, amma duk da haka Derek da matarsa Lydia sun kasance da aminci ga kiran da Allah ya yi masu.

A shekara ta 1968, hidimar koyarwa ta Derek ta bunkasa sosai a tsakanin mutanen da ke da ra'ayin falkawa, da ke tasowa. Ya yi tafiye tafiye da yawa, yana wa'azin Kalmar Allah da karfi da iko.

Lydia Prince ta rasu ranar 5 ga watan Oktoba, shakara ta 1975, kewaye da dangi. Tana mai shekara 85 da ta rasu. Ita ce marubuciyar littafin nan mai suna "Alƙawari a Urushalima" wanda aka wallafa kafin mutuwarta a wannan shekarar.

Ruth Prince

A cikin shekara ta 1978, Derek ya auri matarsa ​​ta biyu, mai suna Ruth Baker, 'yar kasar Amurka , mai ‘ya’ya uku da ta ke riko. Sun hadu ne a Urushalima sa’ad da Derek ya ziyarci Isra’ila tare da abokan sa.

Wani sabon salon hidima ya fito a lokacin da suka ƙaddamar da wani shiri na rediyo mai take "Yau tare da Derek Prince". An fara watsa wannan shirin a gidajen rediyo guda takwas, nan da nan masu sauraro suka karu kuma aiki ya kara inganta. A yau, an rarraba waɗannan nadin fayafan koyaswar sa a duk faɗin duniya kuma ana samun su cikin yare iri-iri

An rubuta cikakkun bayanai game da labarin soyayyar Derek da Ruth a cikin wani littafi mai suna “Allah Mai Hada Aure” wanda suka rubuta tare, kuma suka wallafa a shekara ta 1986.

Derek da Ruth Prince sun dauki hoto kusa da Kogin Zambezi, Zambia, a cikin shekara ta 1985.

Ruth ta rasu a Urushalima a ranar 29 ga watan Disamba 1998 bayan 'yar gajeruwar rashin lafiyar da ba a fahimce ta ba. Ta na da shekaru 68 kuma ta yi hidima da aminci tare da mijin ta Derek sama da shekaru ashirin.

Cike da baƙin ciki, wani kololon bacin rai ya fara tasowa a cikin zuciyar Derek. Da ya fahimci cewa wani kazamin ruhu ne ke son ya nisanta shi da Allah, sai ya yi sanarwa a gaban jama’a ranar jana’izar Ruth, da za ta ayyana sauran rayuwar sa. Sa’ad da ake sauke akwatin zuwa cikin ramin, Derek ya gode wa Allah don dukan abin da ya yi a rayuwar Ruth, yana tabbatar da sahihiyar ƙaunar sa da kuma dogara ga Ubansa na sama . Da yake tunawa da wannan lokacin, daga baya ya ce:

“Lokaci ne mai mahimmanci a rayuwata. Na san ba zan iya ci gaba da baƙin cikin da nake ji game da Ruth ba. In na ci gaba haka , a koyaushe zan zargi Allah, yin haka kuma zai chuta ma rayuwata. Wannan ita ce kadai mafita a gareni.”

Mutuwa

Derek Prince ya rasu bayan ya kai karshen kwanankin sa ranar 24 ga Satumba 2003, yana da shekaru 88. Ya sha fama da rashin lafiya na tsawon lokaci kuma ya rasu a cikin barci a gidansa a Urushalima.

An binne shi a makabartar International Church a Urushalima. Ga abin da aka rubuta akan Dutsen kabarin Derek:

DEREK PRINCE
1915-2003
YA TAFI GIDA
Malami mai koyarda Maganar Allah.
Cikin Gaskiya da Bangaskiya da Kauna
Waɗanda ke cikin Almasihu Yesu domin dukan mutane.
Allah mai Aminchi

Derek Prince lokacin da yake wa'azi a Trinity Church (yanzu Cornerstone Church) a San Antonio, Texas, a shekara ta 1974.

Malamin Littafi Mai Tsarki

A shekara ta 1944, yayin da yake aiki a wurin ajiyar magunguna a Kiriat Motzkin, Isra'ila, Ubangiji ya yi magana da Derek a sarari yana cewa:

"An kira ka ka zama malamin koyarda Nassi cikin gaskiya da bangaskiya da ƙauna, waɗanda ke cikin Almasihu Yesu - ga mutane da yawa."

Maganar ta yi kamar abin da ba zai taba faruwa ba, amma a cikin lokaci ta kasance kamar yadda Allah ya yi alkawari a cikin 1941:

“Zai zama kamar kankanin rafi. Rafin zai zama kogi. Kogin zai zama babban kogi. Babban kogin zai zama teku. Tekun za ta zama babban teku, zai kasance ta wurinka. Amma ta yaya? ba za ka sani ba, ba lallai ka iya sani ba, ba za ka sani ba."

Har ila yau, sunan Derek Prince ya kasance cikin masu koyasda tauhidi da inganci da kuma koyarda maganar Allah a zahiri. Bangaskiyarsa da kuma sadaukarwarsa ga yin nazarin nassosi sun sa ya zama ɗaya daga cikin malaman Littafi Mai Tsarki da aka fi darajantawa da kuma ake ganin sha’awarsu a zamaninsa.

Derek marubucin litattafai ne na sama da 100 da kuma tarin takardun koyarwar Littafi Mai-Tsarki wanda ke dawwama aikinsa da yayi . An fassara su zuwa harsuna sama da 100, kuma sun kasance tushen ƙarfafawa da nazari ga masubi da yawa a duk koi'na a faɗin duniya.

Shekara guda kafin rasuwar Derek a shekara ta 2003, wani ɗan jarida na gidan Jarida na Urshalima ya tambaye shi menene bukatar ekklisia mafi girma a yau. "Malaman Littafi Mai Tsarki," in ji Derek, "masu koyar da Littafi Mai Tsarki." Da yake tunawa da tattaunawar, ɗan jaridar ya rubuta a cikin 2006, "Hakika, malamai kamarsa kalilan ne."

Derek Prince Ministries

A cikin Mayu 1971, Derek ya buɗe ma'aikata a Fort Lauderdale, Florida, domin wallafawa da rarraba koyarwarsa. Asalin dai an fi sanin wurin da suna Derek Prince Publications. Da ayyuka suka fadada, aka sake sunan zuwa Derek Prince Ministries a cikin watan Disamba 1990.

A yanzu, Derek Prince Ministries na da ma'aikata a ƙasashe sama da 45 a faɗin duniya, gami da Australia, Kanada, China, Faransa, Jamus, Netherlands, New Zealand, Norway, Kasar Rasha, Afirka ta Kudu, Switzerland, Burtaniya da Amurka. Wannan kungiya A tsaye ta ke domin ciyar da masu fama da yunwa ta ruhaniya, kuma ta yin haka, na ƙarfafa kira da hangen nesan da Derek ya ambata a watan Yuli shekara ta 2002:

“Buri na ne, kuma na gaskanta muradin Ubangiji ne, cewa wannan hidima ta ci gaba da aiki, wanda Allah ya fara ta wurina sama da shekaru sittin da suka shige, har sai Yesu ya dawo.”
Game da Derek Prince | Derek Prince Ministries Nigeria (2024)
Top Articles
Latest Posts
Article information

Author: Carmelo Roob

Last Updated:

Views: 6425

Rating: 4.4 / 5 (45 voted)

Reviews: 84% of readers found this page helpful

Author information

Name: Carmelo Roob

Birthday: 1995-01-09

Address: Apt. 915 481 Sipes Cliff, New Gonzalobury, CO 80176

Phone: +6773780339780

Job: Sales Executive

Hobby: Gaming, Jogging, Rugby, Video gaming, Handball, Ice skating, Web surfing

Introduction: My name is Carmelo Roob, I am a modern, handsome, delightful, comfortable, attractive, vast, good person who loves writing and wants to share my knowledge and understanding with you.